Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce ci gaban kasar Sin ba zai iya rabuwa da duniya ba, kuma ci gaban duniya yana bukatar kasar Sin. Kaza lika kasar Sin za ta ci gaba da samar da wani yanayi na kasuwancin kasa da kasa da ya dace da kasuwa, kuma bisa doka, kana za ta raba kasuwannin ta da rabe-raben da ake samu wajen bude kofa, tare da kamfanonin sassan duniya.
Mao ta bayyana haka ne a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Jumma’a ranar 26 ga wata.
Rahotanni na cewa, yayin bikin bude taron koli na bunkasa harkokin cinikayya da zuba jari na duniya na shekarar 2023, wanda aka gudanar kwanan baya, mahalarta taron masu yawa, suna da kyakkyawan fata game da makomar tattalin arzikin kasar Sin, sun kuma bayyana cewa, yanke huldar kasuwanci zai kawo karin nauyi ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Bugu da kari, shugaban kwamitin gudanarwa na kamfanin Siemens na kasar Jamus, da babban jami’in zartaswa na kamfanin Nvidia, wani kamfanin kera sassan na’urorin laturoni na Chips na kasar Amurka, su ma sun bayyana a cikin wata hira da aka yi da su a baya-bayan nan cewa, ba za a iya maye gurbin kasuwannin kasar Sin ba, kuma ficewa daga kasuwannin kasar Sin ba abu ne mai yiwuwa ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)