Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Jumma’a 14 ga wata cewa, kasar sa na mai da hankali sosai kan batun basussukan kasashe masu tasowa, kuma tana tsayawa tsayin daka kan matsayinta game da batun.
Wang Wenbin ya ce, kasar Sin ta gabatar da shawarwari guda uku, a gun zaman tattaunawa kan batun basussuka na kasa da kasa da aka yi kwanan nan.
Sin na ganin cewa, da farko, masu lamuni na bangarori daban-daban ya kamata su gaggauta gabatar da wani shiri mai nagarta, yayin da suke shiga harkokin warware matsalar bashi. Na biyu, ya kamata asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya hanzarta inganta nazarin kyautata dabarun biyan bashi da musayar bayanai. Na uku, ya kamata bangarori daban daban su gaggauta cimma ra’ayin bai daya, kan yadda za a baiwa masu ba da lamuni damar shiga a dama da su wajen sauke bashi.
Wang Wenbin ya bayyana fatan sa cewa, dukkan bangarorin za su aiwatar da tsarin hadin gwiwa, na tinkarar harkokin basussuka dake biyo bayan shawarar kawar da basussuka, da kuma warware matsalolin basussukan yadda ya kamata a dukkan fannoni. (Mai fassara: Bilkisu Xin)