Yau 7 ga watan Yuli ake cika shekaru 87 da kutsen Japan a kasar Sin da ake kira da lamarin Gadar Lugou, wanda ya faru a rana mai kamar ta yau a shekarar 1937. Ranar tana da muhimmanci cikin tarihin kasar Sin, inda a ranar ce Japan ta kutsa cikin kasar Sin daga dukkan fannoni yayin yakin duniya na II. An gudanar da shirye shirye a fadin kasar domin kara nanata kudurin kasar Sin na neman ci gaba cikin lumana.
Yakin bijirewa kutsen Japan ya gudana daga shekarar 1931 zuwa 1945. Yakin ya haifar da wahalhalu tare da tagayyara ga al’ummar Sinawa. Alkaluma a hukumance sun nuna cewa, sojojin Sin da fararen hula sama da miliyan 35 ne suka mutu yayin yakin, adadin da ya dauki kusan kaso 8 na daukacin al’ummar Sinawa a shekarar 1928.
- Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Tajikistan Zai Haifar Da Sabuwar Makoma
- Wang Yi: Ziyarar Xi Ya Zurfafa Dangantakar Kasashe Makwabta
A kowacce shekara, a kan gudanar da shirye-shirye a kasar Sin domin tunatar da illolin yaki da muhimmancin zaman lafiya.
Kasar Sin ta dauki gomman shekaru ta na bin tafarkin samun ci gaba cikin lumana, inda take fafutukar gina al’umma mai karko da wadata yayin da take kokarin kulla kyakkyawar dangantaka da sauran kasashen duniya. (Fa’iza Mustapha)