A ranar 7 ga wata ne kasar Amurka ta yi shelar sake kara dora wa kayayyakin kasar Sin haraji na kaso 50 tun daga ranar 9 ga wata, muddin kasar Sin ba ta soke matakin kakaba haraji na kaso 34 kan kayayyakin Amurka kafin ranar 8 ga wata ba, lamarin da ya shaida wa duniya mummunan nufin Amurka na neman samun abin da bai dace ba da kuma barazara. Duk da haka, Amurka ba za ta cimma burinta ba. kasar Sin ta bayyana cewa, idan Amurka ta ci gaba da matakinta, to ita ma ba za ta ja da baya ba.
Tun bayan barkewar yakin cinikayya da Amurka ta ta da kan kasar Sin a shekarar 2018, tattalin arzikin kasar Sin ya kara juriya. Kasar ta fadada yin cinikayya da kasashen duniya. Tun bayan shekarar 2018, inda yawan kayayyakin da take fitarwa zuwa ASEAN da kasashen da suke aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ya karu, yayin da yawan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka ya ragu. Ma iya cewa, yadda Amurka take kakaba haraji kan kayayyakin kasar Sin ba zai yi illa sosai kan tattalin arzikin kasar Sin ba.
- Sin Za Ta Mai Da Martani Kan Barazanar Kara Kakkaba Mata Harajin Kwastam Daga Amurka
- Kyautar LEADERSHIP Ta Kara Zaburar Da Mu Kan Sauke Nauyin Al’ummar Jigawa Akanmu – Gwamna Namadi
Ban da haka kuma, a kwanan baya, wasu hukumomin hada-hadar kudi masu jarin waje sun kyautata hasashen da suka yi kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na bana, kana wasu kamfanonin kasa da kasa ciki had da na Amurka da dama sun ayyana kasar Sin a matsayin wurin da aka samu tabbaci ta fuskar zuba jari da habaka ciniki, inda suka nuna cewa, za su ci gaba da fadada hadin gwiwa da zuba jari a kasar Sin da kuma zurfafa ciniki a kasuwar kasar Sin.
Duk da matsin lambar da Amurka ke yi, kasar Sin tana da dabararta, za ta ci gaba da mai da hankali kan ayyukanta, za ta kuma rika bude kofarta ga ketare. Har kullum kasar Sin na ganin cewa, ainihin huldar da ke tsakaninta da Amurka ita ce samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare. Ya kamata a daidaita sabanin ciniki ta hanyar tattaunawa cikin adalci. Amma idan Amurka ta fara dora harajin da ta yi shelar dauka, to, kasar Sin za ta dauki wajibabbun matakai, domin kiyaye halastattun hakkokinta. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp