Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Litinin ranar 20 ga wata cewa, kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya, da su fuskanci kiran da kasashen duniya suke yi na tabbatar da adalci, da dage takunkumi kan bangare daya, kana da mutunta hakkin dan adam na wasu kasashe, da dokokin kasa da kasa.
Rahotanni sun ce, a kwanan baya, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan batun matakan tilastawa kan bangare daya, Du Han, ya fitar da wata sanarwa, inda ya nuna damuwa kan matakan tilastawa bangare daya da Amurka ta dauka, ciki har da sanya takunkumin hana shiga kasar, da kuma daskarar da kadarori a kan daidaikun mutane, da sassan da ke wajen kasar, wanda hakan ya take hakkin bil’adama, kamar su ‘yancin aiki, da ‘yancin tafiya, matakan da ba su dace da ka’idojin kare hakkin dan adam na duniya ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp