Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Jumma’a 16 ga wata cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka ta gaggauta gyara aika-aikar da take tafkawa ita kadai a bangaren kariyar cinikayya da cin zarafi, da kuma daina kassara kamfanonin fasahar kere-kere na kasar Sin da na masana’antar kirkirarriyar basira, watau AI.
A cewar rahotannin da aka bayar, a kwanan nan ne ofishin kula da masana’antu da tsaro na ma’aikatar kasuwancin Amurka ya ba da sanarwa game da amfani da sassan na’urorin laturoni na Chips na Ascend kirar kamfanin Huawei, a matsayin abin da ya keta ka’idar fitar da kaya zuwa waje daga Amurka, tare da gargadi ga jama’a a kan su kiyayi bari ana amfani da fasahar chips ta AI ta Amurka wajen bayar da horo ga nau’o’in fasahar kirkirarriyar basira na kasar Sin.
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun ma’aikatar, Lin Jian, ya shaida wa taron manema labarai na yau da kullum cewa, Amurka ta wuce gona da iri kan batun tsaron kasa da yin amfani da ka’idar fitar da kayayyaki waje ba bisa ka’ida ba, da tsarin shari’a na yanke hukunci ga bakon da ke wajen kasa, domin toshe hanya da kassara kayayyakin fasaha na chip da na masana’antar kirkirarriyar basira ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.
Ya ce, irin wannan aika-aika ta saba wa ka’idojin gudanar da kasuwanci, da kawo cikas ga bangaren sarrafa kayayyaki da tsarin samar da su a duniya, da keta hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin.
Lin ya kara da cewa, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai don kare hakkokinta na samun ci gaba, da kiyaye ‘yanci da muradun kamfanonin kasarta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp