Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga kungiyar kasashen G20 da ta zama karfin da ke ingiza tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Wang Yi ya yi kiran, yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi jiya, a Johannesburg na Afrika ta Kudu.
- Ɗanyen Mai Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Ƙaru A Watan Janairun 2025 –OPEC
- Masu Sana’ar Kamun Kifi Sun Koka Kan Ƙarancin Kuɗaɗen Shiga A Taraba
Ministan ya ce, yayin da ministocin harkokin wajen G20 suka hadu, ya zama wajibi a waiwayi yarjeniyoyin da aka cimma a taron Rio de Janeiro, a hada hannu a matsayin karfin ingiza zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, a kuma samar da aminci a duniya, yana mai cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen ganin tabbatuwar hakan.
Da yake tsokaci game da rikicin Ukraine, ministan ya ce kofar samun zaman lafiya na budewa, yana mai jaddada cewa har kullum, kasar Sin ta kasance mai goyon bayan warware rikici da wuri kuma ta hanyar lumana, kana za ta ci gaba da taka rawar gani wajen warware takaddama a siyasance.
Game da batun Gaza kuwa, Wang Yi ya yi kira da a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai inganci, tare da nanata kafa kasashe biyu a matsayin mafita daya tilo ga rikicin.
Bugu da kari, ministan ya ce bana lokaci ne na Afrika, duba da cewa za a gudanar da taron kolin G20 a nahiyar Afrika a karo na farko tun bayan da AU ta zama cikakkiyar mamba.
Ya ce ya kamata a saurari kiraye-kirayen nahiyar, a kuma yi la’akari da damuwarta, kana a taimakawa ayyukanta da samar da damar wanzar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa, kasar Sin na goyon bayan jama’ar nahiyar su warware matsalolin da kansu, kuma tana adawa da kasashen waje su rika tsoma baki cikin harkokin kasashen Afrika. (Fa’iza Mustapha)