Kididdigar da ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun bana, adadin yarjejeniyoyin da suka shafi fasaha da aka kulla ya kai dubu 228 a kasar Sin, wadanda suka shafi Yuan triliyan 1 da biliyan 600, adadin da ya karu da kaso 13.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Lamarin da ya nuna cewa, kasuwar fasaha ta kasar Sin tana bunkasuwa yadda ya kamata.
A matsayin daya daga cikin muhimman kasuwanni 5 na kasar Sin, bunkasuwar kasuwar fasaha tana da muhimmanci ga aikin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sana’o’i. Kididdigar ta nuna cewa, a shekarar 2024, jimillar kudaden da aka samu daga kulla yarjejeniyoyin fasaha ta kai Yuan triliyan 6 da biliyan 800, adadin da ya karu da kaso 11.2 bisa dari. Lamarin da ya nuna cewa, adadin ya ci gaba da karuwa cikin shekaru 8 a jere, hakan ya sa, kasar Sin ta kai ga cimma burinta a fannin kulla yarjejeniyoyin fasaha, da darajarsu ta kai Yuan triliyan 5, bisa shirin raya kasuwar fasaha tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2025. (Mai Fassara: Maryam Yang)














