Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta daukaka kara zuwa kungiyar cinikayya ta duniya WTO kan hukuncin karshe game da matakin da kungiyar Tarayyar Turai EU za ta dauka kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin a yau Litinin.
Kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na adawa da matakin karshe na kungiyar EU na kakaba haraji kan motoci masu amfani da lantarki kirar kasar Sin bisa hujjar yadda kasar Sin ke samar da rangwame kan motocin, duk kuwa da yawan korafe-korafe da bangarorin da abin ya shafa suka yi, ciki har da gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar EU, da masana’antar motoci da jama’a.
Kakakin ya kara da cewa, don kiyaye muradun bunkasa masana’antar motoci masu amfani da lantarki, da hadin gwiwar duniya kan sauyi zuwa amfani da ababen hawa mara gurbata muhalli, Sin ta yanke shawarar daukaka kara zuwa tsarin sasanta rikici na WTO. (Yahaya)