A yau Talata ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani mai taken tsarin doka da matakan yaki da taaddanci na kasar Sin”.
Takardar ta bayyana taaddanci a matsayin abin ki ga dukkan bilAdama, wanda ke haifar da babban barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, kuma ya kasance kalubale ga dukkan kasashe da dukkan bilAdama, ya zama dole dukkan kasashen duniya su yaki da taaddanci.
- Xi Ya Amsa Wasikar Da Daliban Kenya Da Suka Yi Karatu A Jami’ar Beijing Jiaotong Suka Rubuta Masa
- Gwamnatin Tarayya Ta shirya Kaddamar Da Shirin Baiwa Dalibai Bashi
A shekarun da suka gabata, kasar Sin ta bullo da hanyar yaki da ta’addanci bisa dokar da ta dace da hakikaninta ta hanyar kafa tsarin doka mai inganci, da sa kaimi ga aiwatar da doka mai tsauri, bisa rashin son kai, da tabbatar da gudanar da adalci ba tare da nuna son kai ba, da kiyaye hakkin dan Adam yadda ya kamata, a cewar takardar.
Takardar aikin ta kara da cewa, yayin da ake kiyaye ra’ayin alummar duniya mai makomar bai daya, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da sauran kasashe don ciyar da harkokin yaki da ta’addanci gaba a matsayin wani bangare na gudanar da harkokin duniya.
Game da wannan takardar bayani, kakakin maaikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau da yamma cewa, Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen yaki da taaddanci, da shiga ayyukan yaki da taaddanci na duniya, da yin koyi da muamala da juna bisa tushen girmamawa da nuna adalci ga juna, da sa kaimi ga raya shaanin yaki da taaddanci na duniya, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan duniya.
A gun taron manema labaru na yau da kullum Talatar nan, Wang Wenbin ya bayyana cewa, a matsayinta na wadda ta taba fuskantar illar taaddanci, kasar Sin ta dade tana fuskantar barazanar taaddanci. A cikin shekaru da suka gabata, kasar Sin ta yi cikakken bayani kan dokoki, da halaye, da aikinta na yaki da ta’addanci, da koyi daga wasu kasashe, da tsara wata hanyar yaki da taaddanci bisa doka dake dacewa da yanayin kasar, hakan ya tabbatar da tsaron kasa, da na zamantakewar alumma, da kuma tsaron rayuwa da dukiyoyin jamaar kasar, kana ta samar da gudummawa wajen tabbatar da tsaro a duniya da yankuna baki daya. (Muhammed Yahaya Zainab Zhang)