Babban bankin kasar Sin, ya fitar da wani tsarin amfani da kudin Yuan ta na’ura wato e-CNY, a yunkurinsa na baya-bayan nan, na saukaka biyan kudi ta wayar salula ga baki.
A cewar babban bankin, masu amfani da wayar salula na iya neman manhajar “e-CNY” a kasuwar manhajoji ta App Store ko Google Play, domin sauke manhajar da kuma sanya tsarin amfani da yuan ta naura, sannan su yi regista domin samun asusu. Daga nan sai a danna inda aka rubuta “Open/Add e-CNY Wallets” wato bude jakar kudi ta wallet, sai a zabi hanyoyin biyan kudin da aka sahalewa bayar da hidimomi ga baki domin kammala registar, kana a fara amfani da jakar kudi ta e-CNY Wallet.
- CMG Ya Kaddamar Da Wani Shirin Yayata Labaran Kasar Sin Da Al’ummun Kasa Da Kasa Za Su Iya Shiga
- An Nuna Dandanon Shirye-Shiryen Bikin Sabuwar Shekarar Sinawa Na CMG A Filin Jiragen Sama Da Yankunan Kasuwanci Na Dubai
Sanarwar da bankin ya fitar a jiya, ta ce za kuma a iya yin registar jakar kudi ta e-CNY Wallet ne ta hanyar amfani da lambobin waya na kasashe da yankuna sama da 210.
A farkon watan nan ne kuma tsare-tsaren biyan kudi ta wayar salula na manyan manhajojin biyan kudi na kasar Sin wato Alipay da WeChat suka sanar da cewa, a yanzu baki za su iya hada katunan karbar rance na bankunan kasashen waje, wato Credit Card da manhajojin, kuma katunan sun hada irin na Visa da Master. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp