Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda a ranar Litinin, ya sanar da raba fiye da Naira miliyan 470 ga wadanda ta’addancin ‘yan bindiga da cutar korona (COVID-19) ya shafa a jihar.
Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Ibrahim Mohammed, ya fitar, ta bayyana cewa, an kaddamar da shirin ne tare da hadin gwiwar Hukumar Ba da Agaji ta Duniya da kuma R.H. Equipt, da nufin rage wahalhalun tattalin arziki da wadannan kalubalen ke haifarwa.
- Gwamnatin Zamfara Za Ta Zamanantar Da Asibitin Kwararru Na Yeriman Bakura Da Daga Darajarsa
- Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga, Kachalla Damina Da Yaransa
A yayin bikin kaddamar da shirin da aka gudanar a dakin taro na Kabir Aliyu Maska da ke babban birnin jihar, Gwamna Radda ya bayyana cewa, wadanda ta’addancin masu garkuwa da mutane ya rutsa da su, su 550 za su karbi Naira 150,000 kowannensu, yayin da mutane 3,876 wadanda suka kamu da cutar COVID-19 suka samu N100,000 kowannensu.
Wannan ya kawo jimillar kudin da aka kashe zuwa Naira miliyan 470, ban da kudin da aka kashe kan horaswar da aka yi wa wadanda suka ci gajiyar shirin a fadin kananan hukumomin Katsina 34.