Kwanan nan, ma’aikatar aikin gona da raya kauyuka ta kasar Sin, ta gabatar da shirin ci gaba da zamanantar da bangaren aikin gona a kasar, cikin shekaru 4 masu zuwa.
Wannan shiri, zai fi mai da hankali kan wasu muhimman bangarori, da ayyuka masu alaka da zamanantar da aikin gona, wanda ya shafi matakan da suka hada da gagauta samar da wasu kayayyakin samar da hidimomi ga jama’a. Alal misali akwai wani cikakken tsarin samar da alkaluma, don nuna yanayin da ake ciki a fannin raya aikin gona da kauyuka, da kafa dimbin gandayen noma, da makiyaya, da yankin teku na kiwon kifi, masu kunshe da fasahohin zamani, gami da aikin gudanar da gwaje-gwajen sabbin fasahohin aikin gona, a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, da tantance damammakin amfani da fasahar zamani daban daban.
Kana a bisa shirin da aka gabatar, daga yanzu har zuwa karshen shekarar 2028, za a yi kokarin cimma burikan da suka kunshi inganta ayyukan samar da hidimomi ga jama’a ta fasahohin aikin gona na zamani, da sanya fasahohin zamani taka rawar gani a fannin samar da karin amfanin gona, da tabbatar da kammalar aikin zamanantar da daukacin tsare-tsaren aikin gona a wuraren da ake aiwatar da gwaje-gwajen fasahohi, da samun ingantaccen tsarin da zai tabbatar da samun nasara a yunkurin zamanantar da aikin gona a duk fadin kasar, gami da samun jimillar ma’aunin ingancin zamanantarwar bangaren aikin gona da ta kai fiye da kaso 32%. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp