Da safiyar yau Talata ne ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya kira taron manema labarai na ciki da wajen kasar Sin, a gefen taron majalisar wakilan jama’ar kasar karo na 14 dake wakana.
Minsitan ya ta amsa tambayoyi da dama da suka shafi kasar Sin da manufofi da dangantakarta da kasashen waje.
Dangane da zamanintar da kasar Sin, Qin Gang ya ce zamanantarwar ta Sin, ta samarwa duniya mafita dangane da kalubalen da take fuskanta. Tabbas nasarorirn da Sin ta samu sun shaida cewa, kowace kasa na da damar zabarwa kanta hanya mafi dacewa da ita. Hakika Sin ta zama abun misali ga sauran sassan duniya, domin ta bugi kirji ta yi abun da babu wata kasa da ta taba yi. Ta kasance kasa daya tilo da ta kai matakin da take yanzu, ba tare da mulkin mallaka ko danniya ba, lamarin da ya cancanci yabo ainun kuma ya dace a yi koyi da shi. Ta kuma nuna wa duniya wata tsaftattaciyar hanyar samun ci gaba mai dorewa.
Ya kuma amsa tambaya game da dangantakar Sin da Amurka. Yana mai cewa, ya kamata Amurka da Sin su hada hannu wajen mayar da dangantakarsu bisa turba. Kamar yadda ministan ya fada, idan har Amurka ta ci gaba da takala, to za ta haifar da fito-na-fito da tsamin dangantaka.
Lallai ya kamata Amurka ta gane cewa, babu wani matsin lamba ko yada jita-jita da zai kai ga dakile ci gaban kasar Sin, domin salonta na raya kai, ya fi mayar da hankali ne kan albarkatunta na cikin gida, kuma tubalin ci gabanta na da karfi, don haka da wuya a iya dakile ci gaban da ta samu. Haka kuma, kasuwar kasar Sin mai bude kofa, dama ce ga kamfanonin Amurkar da ma na sauran sassan duniya, don haka, bita da kulli ba zai kai Amurka ga cimma burinta na dakile Sin ba, sai ma dai ta dakile ci gaban kamfanoninta.
Dangane da dangantakar Sin da Rasha da ma rikicin Ukraine, ya ce dangantakar Rasha da Sin ba ta zama barazana ga kowa. Dangantaka ce ta mutuntawa da moriyar juna. A ganina irin dangantakar Sin da Rasha, ita ake bukata tsakanin kasa da kasa musamman ma manyan kasashe, domin zama abun misali. Dangantaka ce irin ta girmama juna da mutunci, wadda babu katsalandan ko neman ganin faduwar wani banagre.
Game da rikicin Ukraine kuwa, ministan ya ce bai kyautu a yi wa Sin barazana ko kakaba mata takunkumi ba. Sam neman da ake yi na shafawa Sin bakin fenti dangane da rikicin bai dace ba, domin ta kasance mai kira da yin sulhu da tsagaita bude wuta. Haka kuma ba mu taba jin inda aka ce Sin din ta bayar da gudunmuwar wani abu ga wani bangare a rikicin ba.
Wannan shi ne halin dattako da sanin ya kamata, kuma haka ya kamata duk wata babbar kasa, da take neman zaman lafiyar duniya da gaske ta yi. (Fa’iza Mustapha)