Kamfanin hakar mai a teku na kasar Sin wato CNOOC ya sanar a yau Jumma’a cewa, a kwarin dake bakin kogin Zhujiang a tekun Nanhai na kasar Sin, an gano filin hakar mai na farko a cikin ruwa mai zurfi, wanda ake kiransa filin hakar mai na Kaipingnan, wanda yawan mai da iskar gas da za a iya hakowa a wurin ya kai ton miliyan 102 baki daya.
Filin hakar mai na Kaipingnan yana kwarin Kaiping a gabashin yankin tekun Nanhai, nisan da ke tsakaninsa da birnin Shenzhen ya kai misalin kilomita dari 3, matsakaicin zurfin ruwan kuma ya wuce mita dari 5, kana tsawon rijiyar hakar mai mafi zurfi ya kai mita 4831. Za a iya haka danyen mai irin na danyen mai maras nauyi a wurin. Har ila yau zurfin kasar da aka gano iskar gas a ciki ya kai mita 100.6. Sakamakon jarrabawar da aka yi ya nuna cewa, matsakaicin yawan mai da iskar gas da za a iya hakowa a kowace rana ya wuce ton 1000, adadin da ya kafa tarihi a wannan fanni a kasar Sin. (Tasallah Yuan)