Bisa labarin da aka labarta daga hukumar makamashin nukiliya ta Sin a yau Jumma’a, an ce, tawagar kwararru ta Sin ta gano ma’adanin Yuraniyom mafi daraja a karkashin kasa da ya kai zurfin mita 1,820 a yankin Tarim dake jihar Xinjiang, inda hakan ya kafa sabon tarihi na wuri mafi zurfi da aka gano ma’adanin Yuraniyom mafi daraja, ya kuma shaida yadda Sin ta kasance kan gaba a fannin ganowa da binciken albarkatun ma’adanin Yuraniyom mafi daraja a tsakanin kasa da kasa.
An ba da labari cewa, wannan binciken zai taka rawa sosai a aikin hako Yuraniyom mafi daraja da kasar Sin ke yi, kuma zai kara habaka karfin aikin hako ma’adinan Yuraniyom mafi daraja da kasar Sin ke da shi a yankunan da hamada ta mamaye.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp