Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana a yau Juma’a cewa, yayin da kasar Sin ke maraba lale da ziyarar da dan majalisar dattawan Amurka Steve Daines ya kawo kasar, har ila yau kasar tana kyakkyawar maraba ga mutane daga dukkan sassan Amurka, ciki har da ‘yan majalisar dokokin kasar masu aniyar kawo ziyara.
An ba da rahoton cewa, dan majalisar dattawan Amurka na jam’iyyar Republican, Steve Daines ya sauka birnin Beijing a ranar Alhamis. Mao ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa a-kai-a-kai, sa’ilin da aka nemi jin abin da ake tsammani game da ziyarar ta Daines.
- Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
- Girgizar Kasa: Shugaban Kasar Myanmar Ya Mika Godiya Ga Tawagar Likitocin Yunnan Ta Kasar Sin
Mao ta ce, kasar Sin ta yi imanin cewa, samun kwanciyar hankali, da kyakkyawar alaka da ci gaba mai dorewa a huldar Sin da Amurka tana samar da moriya ta bai-daya ga al’ummomin kasashen biyu, kuma ta dace da abin da al’ummomin duniya ke fatan gani.
A wani labarin kuma, an ba da rahoton cewa, an kaddamar da sufurin jirgin kasan jigilar kayayyaki na farko na Beijing da zai rika zirga-zirga tsakanin kasar Sin da yankin tsakiyar Asiya a hukumance kwanan nan. Jirgin jigilar kayayyakin na kasa da kasa, da aka makare da kayayyakin da ake fitarwa waje, ya baro birnin Beijing zuwa Tashkent, babban birnin kasar Uzbekistan.
Dangane da haka, Mao Ning ta ce, a cikin ‘yan kwanakin nan, kasar Sin ta samu ci gaba mai yawa a fannin cudanya da kasashen da ke makwabtaka da ita. Kuma kasar za ta ci gaba da samar da damammaki da neman ci gaba tare da kasashen makwabtanta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp