Yau ranar 15 ga wata, ranar kiyaye muhallin halittu ta kasar Sin ce, ranar da a wannan shekara ta samu jigon “gaggauta sauya salon bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma ta yadda zai zama mai kiyaye muhalli”, kuma an gudanar da babban bikin ranar a birnin Sanming na lardin Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin, inda aka bayyana jerin muhimman nasarorin da aka cimma a wannan fanni.
A gun bikin, jami’in hukumar kula da harkokin raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin, ya ce Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suka fi saurin rage yawan makamashin da suke amfani da shi wajen samar da kayayyaki, kuma ta fi saurin raya makamashin da ake iya sabuntawa a duniya, kana yawan makamashi da ake iya sabuntawa a kasar da Sin din ke samarwa na kan gaba a duniya. Ban da haka, kasar ta kafa cikakken tsarin samar da sabbin makamashi mafi girma a duniya.
A gun bikin na bana, an shirya taron bayyana muhimman nasarorin da aka cimma wajen kiyaye muhallin halittu, da taron kara wa juna sani kan harkokin kiyaye muhalli, da nune-nunen kayayyaki masu nasaba da kiyaye muhalli, wadanda a karo na farko aka gudanar a kasar da sauransu. (Lubabatu Lei)