A jiya ne, kasar Sin ta sake samun ci gaba kan shirin filayen hakar mai da iskar gas na Shunbei. Kamfani tace mai mafi girma na kasar Sin wato Sinopec ya sanar da cewa, zurfin rijiyar mai lamba 84 a sansanin Shunbei da ke doron kasa na Tarim a jihar Xinjiang ta kasar Sin ya zarce tsayin mita 8937.77, hakan ya sanya ta zama rijiyar mai mafi zurfi da aka hako a mike a doron kasa na nahiyar Asiya a halin yanzu. Gwaje-gwajen da aka yi kan rijiyar mai lambar 84, sun tabbatar cewa, rijiyar za ta samar da danyen man fetur da iskar gas da ya kai nauyin ton 1017 a ko wace rana, kwatankwacin tan 496.6 na danyen man fetur da kuma iskar gas da ya kai girman cubic mita dubu 653 a ko wace rana.
Yanzu a wurin hakar mai da iskar gas na Shunbei, akwai rijiyoyi guda 49 wadanda zurfinsu ya wuce mita dubu 8, lamarin da ya alamta cewa, an samu nasarar yin amfani da wurin hakar mai da iskar gas na Shunbei mafi zurfi a duniya.
Wurin hakar mai da iskar gas na Shunbei yana yankin tsakiya maso yammacin kwarin Tarim a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Matsakaicin zurfin wurin da ake samun danyen mai ya wuce mita 7300, lamarin da ya sa wurin na Shunbei zama daya daga cikin takwarorinsa mafiya zurfi a doron kasa na duniya, wadanda aka riga aka haka domin kasuwanci. An ruwaito cewa, yanzu haka kaso 60% na yawan sabbin albarkatun danyen man fetur da iskar gas da aka gano a duniya, sun fito ne daga karkashin kasa mai zurfi. Filayen karkashin kasa masu zurfi da masu matukar zurfi sun kasance inda aka fi samun danyen mai da iskar gas masu yawa. (Tasallah Yuan)