Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin.
Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin Tarim, a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, ta kasance wani gagarumin aiki na binciken kimiyya. Bayan neman albarkatun man fetur da gas, an kuma tsara aikin rijiyar don zurfafa nazarin juyin halittar duniya da kuma zurfafa ilimin binciken kasa.
A cewar kamfanin CNPC, an fara aikin hakar rijiyar ne a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2023, inda aka shafe fiye da kwanaki 580 kafin a kai ga kammala tsawon mita 10,910 na hakar, kana an shafe fiye da rabin lokacin, watau kimanin kwanaki 300 ana fama da aikin hakar tsawon mita 910 na karshe. Rijiyar ta ratsa cikin siffofin yanayin kasa har guda 12, wadda daga karshe ta kai ga isa shimfidadden dutsen da adadin shekarun samuwarsa suka kai tsawon shekaru miliyan 500. (Abdulrazaq Yahuza Jere)