Ma’aikatar kula da albarkatun jama’a da lura da zamantakewar al’umma ta kasar Sin ta sanar a yau Talata cewa, kasar Sin ta samar da sabbin guraben aikin yi a birane miliyan 12.56 a shekarar 2024.
A cewar ma’aikatar, an kaddamar da tsarin fansho na mutum daya a duk fadin kasar, kuma shirin gwaji na kariya daga rauni yayin aiki na sabbin nau’o’in ayyuka ya samu ci gaba mai kyau. Ya zuwa karshen 2024, adadin masu rike da katin inshorar zamantakewa ya kai biliyan 1.389.
Bugu da kari, ta fuskar karfafa gina rukunonin kwararrun ma’aikata masu fasaha da basira, sama da mutane miliyan 12 ne suka samu takardar shaidar kwarewa ko takardar shaidar cancantar zama kwararre a duk shekarar. (Mohammed Yahaya)