A jiya Lahadi ne, lardin Qinghai dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, ya fara aikin gina tashar samar da wutar lantarki da za ta iya adana wutar lantarkin da ya kai kilowatt miliyan 20, abin da ke zama wani muhimmin aiki a yammacin kasar Sin, wanda Allah ya horewa albakartun makamashi mai tsafta.
Ita dai wannan tashar wutar lantarki tana amfani da wutar lantarki ne wajen tura ruwa zuwa wani wuri mai tsayi don adanawa, daga bisani kuma ta saki ruwan don samar da wutar lantarki a lokacin da wutar ba ta wadatar ba.
Ana sa ran aikin da za a gudanar a gundumar Guinan na lardin Qinghai da za a zuba jarin da ya kai kudin Sin Yuan biliyan 16, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.24, ta zama tashar da za ta iya samar da wutar lantarki mafi girma a yammacin kasar Sin.
Sabuwar tashar za ta iya samar da wutar lantarkin da zai iya kaiwa kilowatt miliyan 2.8. Kuma da zarar ta fara aiki, ana kiyasin za ta taimaka wajen rage yawan amfani da gawayi da kusan tan miliyan 1.82 da kuma rage fitar da iskar carbon dioxide da kusan tan miliyan 4.55 a kowace shekara.
Qinghai na sa ran ganin karfin sabuwar tashar samar da makamashin, ya zarce kilowatt miliyan 100 nan da shekarar 2030.(Ibrahim)