A safiyar yau Litinin, hukumar kula da gandun daji da tsirrai ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai, inda ta mai da hankali kan gabatar da yadda aka shawo kan kwararowar hamada da kuma ci gaban aiwatar da shirin gandun dajin kiyaye arewacin kasar Sin.
Tun daga watan Yunin 2023, hukumar kula da gandun dajin ta yi iyakacin kokarinta wajen aiwatar da shirin gandun dajin kiyaye arewacin kasar Sin. A shekarar 2024, an inganta aiwatar da muhimman ayyuka guda 287, kana aka kammala ayyukan samar da gandun daji daban daban mai kadadar hekta miliyan 3.8, inda hakan ya sa aka fara aiwatar da shirin da kafar dama, da kuma ci gaba da inganta yanayin muhalli na wuraren yashi.
- Rundunar ‘Yansandan Katsina Ta Daƙile Yunƙurin Sace Mutane, Ta Ceto Mutane 14
- Netanyahu Ya Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Da Hizbullah
Kasar Sin ta taba zama daya daga cikin kasashen da suka fi fama da kwararowar hamada, amma bayan an gudanar da aikin rigakafi da warware batun kwararowar hamada yau shekaru 40 da suka gabata, musamman bayan babban taron jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kawo yanzu, an inganta kashi 53 cikin dari na kasar da take fama da kwararowar hamada, kuma yanki na hamada da ya ragu da fiye da hekta miliyan 4.3, ya kasance kan gaba a duniya wajen samun raguwar lalacewar kasa, da dakile kwararowar hamada, tare da samun nasarar shiga hanyar rigakafi da warware batun kwararowar hamada iri na kasar Sin.
Har ila yau, Sin ta zama kasa mafi girma a fannin ba da gudunmawa ga kiyaye muhalli da kuma zama abin koyi ga sauran kasashe kan rigakafi da warware batun kwararowar hamada a duniya. (Safiyah Ma)