Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da kubutar da wasu mutane 14 da a yammacin ranar Lahadi.
Lamarin ya faru ne a kauyen Dan’arau da ke kan hanyar Magama zuwa Jibia a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
- Raɗɗa Ya Kaddamar Da Dakarun Tsaro 550 Kashi Na Biyu A Katsina
- Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna Lakurawa Da Ta Fito A Kebbi
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun bude wuta kan wasu motocin kasuwanci guda biyu, yayin da suke yunkurin sace mutanen da ke cikin motocin.
Jami’in ‘yansanda reshen karamar hukumar Jibia (DPO) da ke jagorantar tawagar ‘yansandan, ya amsa kiran gaggawa cikin gaggawa yayin da ‘yansandan suka yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwar tare da kubutar da mutane 14.
Sai dai a yayin artabun, biyu daga cikin mutanen da aka ceto sun samu raunukan harbin bindiga kuma nan take aka garzaya da su asibiti domin yi musu magani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp