An kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan ci gaban kasar Sin a jiya Litinin, inda mahalarta ke ganin cewa ta hanyar ci gaba mai inganci da bude kofarta, ba kokarin samun ci gaba bisa kuzarinta da boyayyen karfinta kadai Sin ke yi ba, har ma da taka rawar gani wajen gaggauta ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
A ko da yaushe Sin kan furta cewa, gabanta ba barazana ba ce, dama ce. A ganina, tabbas haka batun yake domin duk wani ci gaban da Sin take samu, tana gabatar da shi ga duniya domin samar da sabbin dabaru.
- Sin Ta Taka Rawar Gani Ga Bunkasuwar Tattalin Arzikin Duniya
- Kasar Sin Na Maraba Da Abokai ‘Yan Kasuwa Daga Kasashe Daban Daban Da Su Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar
Kamar yadda a kullum kasar ke zama abun misali ko koyi ga sauran kasashe, duk wani ci gaban da Sin ta samu, zai kasance tamkar zaburarwa ne ga kasashen duniya na son koyi da ita domin kada a bar su a baya. Za mu iya cewa, kasar Sin ta kasance jagora kuma ja gaba, wajen lalubowa duniya sabbin hanyoyin samun ci gaba cikin lumana da ma shawo kan matsaloli.
Ci gaban Sin zai ci gaba da kasancewa tabbaci ga sauran kasashe musamman kasashe masu tasowa cewa, su ma za su iya samun ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar zamantakewa kamar na Sin, idan suka nace, suka kuma zabarwa kansu manufofin da suka dace da yanayinsu, kana suka sanya kishin kasa da ruhin sadaukarwa a zukatansu kamar yadda Sin ta yi.
Mun ga yadda al’amura suka tsaya cik a lokacin da annobar COVID-19 ta aukawa kasar Sin. Mun shaida yadda aka samu tsaikon samun kayayyaki da hauhawar farashinsu saboda tasirin COVID-19 a kasar Sin. To kamar yadda aka ga mummunan tasiri a wancan lokaci, haka ci gaban kasar Sin zai haifar da kyakkyawan tasiri ga duniya.
Idan muka duba bangarori kamar na fasahohin zamani, kowa ya san kasar Sin ce ja gaba a wannan fanni, kuma tana samar da sabbin fasahohi kusan kullum a bangarori daban daban da suka shafi rayuwar jama’a da ayyukansu. Misali yadda take ingantawa da zamanintar da aikin gona, abu ne da zai taka rawar gani wajen samar da wadatar abinci a duniya. Motoci masu amfani da lantarki da Sin take samarwa, za su yi matukar amfani wajen rage dogaro da man fetur, da rage dumamar yanayi don samar da kyakkyawan muhallin rayuwa ga bil adama. Haka ma, bude kofarta da take kara yi, wata dama ce ga kamfanonin kasashen waje na cin gajiyar ci gaban kasar da babbar kasuwar da take da ita.
Don haka abun yi shi ne, kasashen dake neman ci gaba da gaske, su daura damara, su shirya, domin kasar Sin za ta lalubo musu sabbin hanyoyin da za su kara samun alfanu.