Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta bayyana a yau Talata cewa, ta ki amincewa da matakin da Amurka ta dauka na kara kamfanonin kasar Sin 11 a cikin “jerin kamfanonin da ta kakaba wa takunkumi” bisa abin da take kira dalilai na soja.
Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, cikin tsawon lokaci, Amurka ta mayar da batun tsaron kasa ya zama gama gari, ta hanyar keta matakan fitar da kayayyaki tare da murkushewa da danne wasu kamfanoni, wanda ya yi mummunar illa ga hakkoki da muradun kamfanonin da abin ya shafa, da kuma lalata tsaro da daidaiton tsarin masana’antu da tsarin samar da kayayyaki na duniya, tare da kawo cikas ga farfadowa da ci gaban tattalin arzikin duniya.
Kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka da ya gaggauta dakatar da ayyukan da bai dace ba, kuma kasar za ta dauki matakan da suka dace don kiyaye hakkoki da muradun kamfanonin kasar Sin. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp