A yau ne, kasar Sin Sin ta lashi takwabin daukar kwararan matakai, don kare ‘yancin kai da cikakkun yankunanta, biyo bayan ziyarar da wata tawagar Amurka ta kai yankin Taiwan na kasar Sin jiya Lahadi.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidwa taron manema labarai cewa, ‘yan majalisar Amurka karkashin jagorancin Sanata Ed Markey sun wuce gona da iri tare da yunkurin kalubalantar manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, yana mai cewa, yunkurin nasu bai taba cimma nasara ba.
Wang ya ce, ziyarar ta ci karo da manufar “Sin daya tak a duniya” da kuma sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma, ta kuma keta ‘yancin kan kasar Sin da cikakkun yankunanta, kuma ta aike da wani mummunan sako ga masu neman ‘yancin kan yankin Taiwan.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana sake yin kira ga bangaren Amurka, da ya martaba manufar “kasar Sin daya tilo a duniya”, da sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da sassan biyu suka cimma, da daidaita batutuwan da suka shafi Taiwan yadda ya kamata, da kuma daina keta manufar “Sin daya tak a duniya”, domin kaucewa kara illata alakar Sin da Amurka. (Ibrahim)