Mukaddashin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya bayyana nasarar da kungiyar Kano Pillar ta samu Kan kungiyar DMD ta Maiduguri da ci 2-0 a zagaye na 16 na cin kofin Aiteo wanda aka gudanar a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi a ranar Asabar, da cewa abin a yaba ne kwarai da gaske.
Kamar yadda Daraktan yada labaran Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano Hassan Musa Fagge ya Shaida wa manema labarai a Kano.
- Salman Rushdie: Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Na Cikin Mawuyacin Hali Bayan Kai Masa Hari
- Wike Ga Atiku : Kar Ka Zarge Ni In Ka Fadi A Zabe
Gawuna ya alakanta wannan nasarar da “Sai Masu Gida” suka samu a wasan kusa da na karshe da cewa abin tarihi ne ga kungiyar da kuma Hukumar gudanarwar kungiyar bisa dabaru, mai da hankali.
Kyakkyawan fata da Jajircewa. “Gwamnatin Jihar Kano karkashin Jagorancin Gwamnan Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Kuma Jama’ar Kano na alfahari da ku bisa kawo wa Kano farin ciki bisa wani abu da zai sa farin ciki da annushuwa.”