Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna matukar jimamin rasuwar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari.
Lin ya shaida wa taron manema labarai na yau da kullum cewa, kasar Sin tana nuna alhini ga gwamnati da jama’ar Nijeriya, da kuma iyalan tsohon shugaban kasa Buhari.
Lin ya kara da cewa, tsohon shugaban kasa Buhari ya kasance wani muhimmin shugaba a Nijeriya, wanda ya jagoranci al’ummar Nijeriya wajen samun gagarumar nasara a kan turbarta ta gina kasa, ya kuma kara da cewa, marigayin ya kasance aminin Sinawa wanda ya ba da gagarumar gudummawa wajen inganta dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeriya, da hadin gwiwar moriyar juna da sada zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp