Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Talata 4 ga wata cewa, kasarta ta nuna matukar rashin jin dadi, gami da babbar adawa, ga yunkurin da wasu kasashe ‘yan kalilan suka yi, na bata sunan dokar tsaron kasa a Hong Kong, tare da yin shisshigi cikin harkokin dokokin yankin.
Rahotannin da aka ruwaito sun ce, ‘yan sandan yankin Hong Kong sun sanar da neman wasu mutane 8 ruwa a jallo, bisa zargin da ake musu, na tada zaune-tsaye a Hong Kong, da nuna adawa ga kasar Sin, al’amarin da ya janyo damuwa, har ma da “Allah wadai” daga kasashen Amurka, da Birtaniya da Australiya.
Mao ta jaddada cewa, harkokin yankin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kana, bai dace sauran kasashe su yi shisshigi a ciki ba. Ya kamata wasu kasashe ‘yan kalilan su girmama ikon mallakar yankin kasar Sin, gami da dokokin yankin Hong Kong, da dakatar da mara baya ga masu tada zaune-tsaye a Hong Kong, da wanke laifin da suka aikata. (Murtala Zhang)