Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong ya bayyana a jiya Laraba cewa, kasar Sin tana matukar bayyana takaicinta da kuma nadama a kan matakin da kasar Amurka ta dauka a baya, kan daftarin kudirin kwamitin sulhun MDD da aka tsara da nufin magance matsalar jin kai a zirin Gaza.
A jawabin da ya yi kan amfani da hawan kujerar na ki a wajen muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Fu ya ce, kasashen duniya sun dade suna yin gagarumin kira na tsagaita bude wuta da dakatar da yakin da ake yi a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin asarar rayukan fararen hula da haddasa masifar tabarbarewar jin kai, inda hakan ke dakushe lamiri da tausayin bil’adama da kuma dokokin kasa da kasa.
Wakilin ya ce, “Sau da yawa, kwamitin sulhu ya yi ta neman daukar matakai, amma Amurka tana tilasta hana hakan sau da dama,” yana mai cewa, “Idan ba domin kariyar da Amurka take bai wa Isra’ila ba, da ba a yi karan-tsaye ga kudurorin kwamitin sulhun ba da kuma keta hurumin dokokin kasa da kasa”. Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yadda Amurka ta yi amfani da hawan kujerar na ki a kan daftarin kudurin ranar 18 ga watan Satumba wanda zai bukaci Isra’ila ta dage dukkan takunkumin da ta sa na hana kai kayan agaji zuwa Gaza cikin gaggawa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp