Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, zuwa karshen watan Satumbar bana, kasar ta yi nasarar farfado da wasu muhimman koguna da tafkuna 88 a fadin kasar, lamarin da ya maido da rayuwar halittu a magudanai da hanyoyin ruwan da suka bushe a tsawon shekaru da dama.
An samu nasarorin hakan ne a karkashin wani shiri na “farfado da babban kogi” a kasa baki daya na shekarar 2022 zuwa ta 2025. An bullo da tsare-tsaren farfadowa na musamman ga kowane kogi da tafki bisa yanayi da kamanninsa.
Manyan nasarorin da aka samu sun hada da wadda aka cimma a Rawayen Kogin wajen kiyaye kwararar ruwa ba tare da katsewa ba har na tsawon shekaru 26 a jere, da babbar hanyar ruwan mashigin Beijing da Hangzhou, wanda ya katse a tsawon karni guda, inda aka dawo da kwararar ruwa a tsawonsa gaba daya har na tsawon shekaru hudu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)