Rahotanni daga kasar Sin na cewa, kasar ta yi nasarar samar adadin sabbin motoci masu amfani da wutar lantarki miliyan 20 jiya Litinin, a birnin Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong, lamarin da yake zama wani gagarumin ci gaba ga bangaren sabbin motoci masu amfani wutar lantarki na kasar.
Mataimakin shugaban zartaswa kuma babban sakataren kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin (CAAM) Fu Bingfeng, ya bayyana cewa, kamfanin GAC Aion New Energy Automobile Co., Ltd ne ya kera motar, bisa ga wannan matsayi, sashen kera sabbin motoci masu amfani da wutar lantarki na kasar, ya shiga wani sabon mataki na ci gaba mai girma, da inganci a duniya, kana ya zama wani muhimmin bangare na tsarin masana’antu na zamani na kasar Sin.
Ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar ce ta sanar da hakan, a yayin bikin murnar kafa wannan sabon bajintan, wanda aka gudanar a birnin Guangzhou.
Babban manajan rukunin kamfanin kera motaci na GAC Group, Feng Xingya, ya ce, tun bayan da kasar Sin ta fara aikin kera sabbin motoci masu amfani da wutar lantarki a shekarar 1992, nasarorin da kasar ta samu wajen raya sashen, ke zama mai matukar ban mamaki, saboda yawan motocin da take samarwa da kuma sayarwa a halin yanzu, dukkansu sun kasance babu kamarsu a duniya na tsawon shekaru 8 a jere. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)