Dan wasan kasar Sin Cao Maoyuan ne ya samu lambar Zinare ta farko yayin gasar wasannin daliban jami’o’i ta kasa da kasa ta lokacin zafi karo na 31 a birnin Chengdu na kudu maso yammacin kasar Sin, a rukunin gasar Nanquan ta Wushu, a yayin da ‘yan wasan nahiyar Asiya suka mamaye dandalin, inda suka lashe dukannin lambobin Zinare, a rana ta farko ta gasar a jiya Asabar.
Kasancewarta daya daga cikin wasanni 3 da ake iya zaba a Chengdu, wannan ne karo na 2 da gasar kokawa ta Wushu ta shiga gasar wasannin daliban jami’o’i ta kasa da kasa, bayan shigarta ta farko a shekarar 2017.
Tawagar kasar Sin ta rike kambunta a gasar da lambobin yabo 3, daya a wasan Nandao ta mata, daya a wasan Changquan ta maza, sai daya a wasan Tajiquan ta mata. Hui Tak Yan Samuei ta yankin Hong Kong na kasar Sin da Nandhira Mauriskha, ‘yar kasar Indonesia ne suka samu sauran lambobin yabo na Zinare a gasar Wushu. (Fa’iza Mustapha)