A baya-bayan nan ne jaridar “Business Day” ta Najeriya, da sauran kafofin watsa labaru na kasar, suka ba da rahoton cewa, kamfanonin harhada magunguna na kasar Sin da ta Najeriya na shirin yin hadin gwiwa, don gina wata masana’antar harhada magunguna da darajarta ta kai dalar Amurka miliyan 100 a jihar Legas.
Akwai wasu muhimman batutuwa game da wannan hadin gwiwa: Na farko, kamfanonin kasar Sin da ke halartar aikin sun kware wajen samar da magungunan cutar kanjamau, kuma manufar gina masana’antar harhada magunguna ita ce inganta dogaro da kai a Najeriya ta fuskar aikin kiwon lafiya, musamman ma a fannin samar da magungunan hana yaduwar cutar kanjamau.
- Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Kwaso ‘Yan Nijeriya Da Ke LebanonÂ
- Shugaba Tinubu Ya Sake Aika Tallafin Buhun Shinkafa 18,500 Kebbi
Abu na biyu kuma shi ne, an samar da shirin kafa wannan masana’anta ne bayan da kamfanonin harhada magunguna na kasar Amurka da na Turai, irin su GSK da Sanofi, suka janye daga Najeriya kwanan nan. Bisa la’akari da hauhawar farashin kayayyaki, da karancin wutar lantarki, da tabarbarewar yanayin zuba jari, da sauran matsalolin da Najeriya ta fuskanta a shekarun nan, kamfanonin harhada magunguna na yammacin duniya sun zabi janye jiki daga kasar, duk da cewa yin hakan ya kara ta’azzara matsalar karancin magunguna a Najeriya.
Daga wannan kwatance na “wani bangare ya fita waje, yayin da wani ya shiga ciki”, za mu iya fahimtar wani abu mai zurfi, wato dalilin da ya sa kasashen Afirka ke maraba da goyon bayan kasar Sin shi ne:
Na farko, kamfanonin kasar Sin sun dace da muhallin Afirka.
Lokacin da kamfanonin kasashen Yamma suka kasa jurewa kuma suka fice daya bayan daya, a nasu bangare kamfanonin kasar Sin na shigowa. Wannan ya nuna karfin kamfanonin kasar Sin, musamman ma a fannonin takaita kudin da ake kashewa, da kuma tinkarar hadari. Wannan ne ya sa sau da dama da kasashen Afirka ke matukar bukatar samun jari, Sinawa ne kadai ke iya ba su goyon baya.
Na biyu, Sinawa na da niyyar biyan bukatun jama’ar kasashen Afirka.
Alkaluma daga Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin Najeriya sun nuna cewa, a yanzu haka akwai mutane miliyan 2 da suka kamu da cutar kanjamau a Najeriya, tare da samun sabbin masu kamuwa da cutar 1,400 a duk mako, sannan cutar ta sa yara miliyan 1.2 zama marayu. Saboda haka, yadda ake taimakawa Najeriya samun karfin samar da magungunan cutar kanjamau, wani mataki ne na adalci, dake samar da taimakon gaggawa ga al’ummar kasar, musamman ma marasa galihu. Yin hakan ya dace da tunanin gargajiya na Sinawa, na mai da adalci a gaban moriya.
Na uku, kasar Sin tana kokarin cika alkawuran da ta dauka.
A gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing na Sin a watan da ya gabata, kasar Sin ta gabatar da “Ayyuka 10 na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka don tabbatar da zamanantarwa”, ciki har da “Aikin hadin gwiwa a fannin lafiya”, wanda ya kunshi sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin don su zuba jari ga harkar samar da magunguna a Afirka, da inganta bangaren kiwon lafiyar jama’a a kasashen Afirka, da dai sauransu. Babu shakka, wannan aiki na gina masana’antar harhada magunguna a Najeriya, mataki ne na aiwatar da manufofin da aka gabatar a taron kolin da ya gudana.
Idan aka kwatanta da dimbin ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wannan aiki na kafa masana’antar harhada magunguna ba wani aiki mai matukar muhimmanci ba ne. Amma duk da haka, an tabbatar da kimar kasar Sin a Afirka ta hanyar gudanar da ire-iren wadannan ayyuka. Suna iya zama wata masana’antar harhada magunguna, ko madatsar ruwa, da layin dogo, da tashar samar da wutar lantarki ta zafin rana, da dai sauransu. Wato abubuwa ne masu amfani da za su taimaki al’ummar kasashen Afirka wajen magance matsaloli, da kuma samar musu da fa’ida ta zahiri. Dalilin da ya sa kasar Sin ke daukar wadannan matakai, shi ne tunaninta na hadin gwiwa da kasashen Afirka ta hanyar nuna gaskiya, da neman samar da hakikanin sakamako, da tabbatar da zumunta da sahihanci. Wannan tunani ya sa ake samun dangantakar hadin gwiwa mai amfanin juna tsakanin Sin da Afirka, har ma ya sa zumuntar dake tsakaninsu karfafa a kai a kai. (Bello Wang)