ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Samu Karbuwa A Afirka Ta Hanyar Samar Da Abubuwa Masu Amfani

by CGTN Hausa and Sulaiman
2 years ago
Afirka

A baya-bayan nan ne jaridar “Business Day” ta Najeriya, da sauran kafofin watsa labaru na kasar, suka ba da rahoton cewa, kamfanonin harhada magunguna na kasar Sin da ta Najeriya na shirin yin hadin gwiwa, don gina wata masana’antar harhada magunguna da darajarta ta kai dalar Amurka miliyan 100 a jihar Legas.

Akwai wasu muhimman batutuwa game da wannan hadin gwiwa: Na farko, kamfanonin kasar Sin da ke halartar aikin sun kware wajen samar da magungunan cutar kanjamau, kuma manufar gina masana’antar harhada magunguna ita ce inganta dogaro da kai a Najeriya ta fuskar aikin kiwon lafiya, musamman ma a fannin samar da magungunan hana yaduwar cutar kanjamau.

ADVERTISEMENT
  • Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Kwaso ‘Yan Nijeriya Da Ke Lebanon 
  • Shugaba Tinubu Ya Sake Aika Tallafin Buhun Shinkafa 18,500 Kebbi

Abu na biyu kuma shi ne, an samar da shirin kafa wannan masana’anta ne bayan da kamfanonin harhada magunguna na kasar Amurka da na Turai, irin su GSK da Sanofi, suka janye daga Najeriya kwanan nan. Bisa la’akari da hauhawar farashin kayayyaki, da karancin wutar lantarki, da tabarbarewar yanayin zuba jari, da sauran matsalolin da Najeriya ta fuskanta a shekarun nan, kamfanonin harhada magunguna na yammacin duniya sun zabi janye jiki daga kasar, duk da cewa yin hakan ya kara ta’azzara matsalar karancin magunguna a Najeriya.

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

Daga wannan kwatance na “wani bangare ya fita waje, yayin da wani ya shiga ciki”, za mu iya fahimtar wani abu mai zurfi, wato dalilin da ya sa kasashen Afirka ke maraba da goyon bayan kasar Sin shi ne:

Na farko, kamfanonin kasar Sin sun dace da muhallin Afirka.

Lokacin da kamfanonin kasashen Yamma suka kasa jurewa kuma suka fice daya bayan daya, a nasu bangare kamfanonin kasar Sin na shigowa. Wannan ya nuna karfin kamfanonin kasar Sin, musamman ma a fannonin takaita kudin da ake kashewa, da kuma tinkarar hadari. Wannan ne ya sa sau da dama da kasashen Afirka ke matukar bukatar samun jari, Sinawa ne kadai ke iya ba su goyon baya.

Na biyu, Sinawa na da niyyar biyan bukatun jama’ar kasashen Afirka.

Alkaluma daga Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin Najeriya sun nuna cewa, a yanzu haka akwai mutane miliyan 2 da suka kamu da cutar kanjamau a Najeriya, tare da samun sabbin masu kamuwa da cutar 1,400 a duk mako, sannan cutar ta sa yara miliyan 1.2 zama marayu. Saboda haka, yadda ake taimakawa Najeriya samun karfin samar da magungunan cutar kanjamau, wani mataki ne na adalci, dake samar da taimakon gaggawa ga al’ummar kasar, musamman ma marasa galihu. Yin hakan ya dace da tunanin gargajiya na Sinawa, na mai da adalci a gaban moriya.

Na uku, kasar Sin tana kokarin cika alkawuran da ta dauka.

A gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing na Sin a watan da ya gabata, kasar Sin ta gabatar da “Ayyuka 10 na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka don tabbatar da zamanantarwa”, ciki har da “Aikin hadin gwiwa a fannin lafiya”, wanda ya kunshi sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin don su zuba jari ga harkar samar da magunguna a Afirka, da inganta bangaren kiwon lafiyar jama’a a kasashen Afirka, da dai sauransu. Babu shakka, wannan aiki na gina masana’antar harhada magunguna a Najeriya, mataki ne na aiwatar da manufofin da aka gabatar a taron kolin da ya gudana.

Idan aka kwatanta da dimbin ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wannan aiki na kafa masana’antar harhada magunguna ba wani aiki mai matukar muhimmanci ba ne. Amma duk da haka, an tabbatar da kimar kasar Sin a Afirka ta hanyar gudanar da ire-iren wadannan ayyuka. Suna iya zama wata masana’antar harhada magunguna, ko madatsar ruwa, da layin dogo, da tashar samar da wutar lantarki ta zafin rana, da dai sauransu. Wato abubuwa ne masu amfani da za su taimaki al’ummar kasashen Afirka wajen magance matsaloli, da kuma samar musu da fa’ida ta zahiri. Dalilin da ya sa kasar Sin ke daukar wadannan matakai, shi ne tunaninta na hadin gwiwa da kasashen Afirka ta hanyar nuna gaskiya, da neman samar da hakikanin sakamako, da tabbatar da zumunta da sahihanci. Wannan tunani ya sa ake samun dangantakar hadin gwiwa mai amfanin juna tsakanin Sin da Afirka, har ma ya sa zumuntar dake tsakaninsu karfafa a kai a kai. (Bello Wang)

Afirka
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti
Afirka
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri
  • Sulaiman
    Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK
  • Sulaiman
    Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA
  • Sulaiman
    Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

MASU ALAKA

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Inganta Kaddamar Da Aikin Kungiyar Hadin Gwiwar AI Ta Duniya Da Wuri

July 17, 2026

Next Post
Wakilin Sin Ya Bukaci A Kyautata Tsarin Duniya Da Gyara Rashin Adalci Da Aka Yi Wa Afirka

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

July 17, 2026
Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

Sin Ta Yaba Da Matakin Amurka Na Kin Tsawaita Dokar Ta-Baci Dangane Da HK

July 17, 2026
Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

July 17, 2026
Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

July 17, 2026
Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

July 17, 2026
Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

July 17, 2026
Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

July 17, 2026
Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.