Kasar Sin ta samu nasarori a fannin ginin sabbin kayayyakin more rayuwa na zamani, lamarin da ya taimaka mata samun ci gaba a bangaren zamantakewa da tattalin arziki a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Zhang Zhihua, jami’in hukumar raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau cewa, kasar Sin ta gaggauta matakanta na sabunta kayayyakin sadarwa da kuma inganta hade ababen more rayuwa da kirkire-kirkire.
Ya ce tsawon layin sadarwa na Optical Fiber ya ninka sau 2.7 cikin shekaru goma da suka gabata, kuma adadin cibiyoyin adanawa da kare bayanai, ya dara miliyan 5.9.
Baya ga haka, ya ce ana amfani da na’urorin zamani a bangarorin sana’o’i da harkokin kasuwanci daban daban kamar na sufuri da samar da makamashi da ayyukan masana’antu, da bangarorin da suka shafi walwalar jama’a kamar cinikayya ta intanet da samun kiwon lafiya da ilimi ta intanet.
A bangaren kirkire-kirkire kuwa, Zhang ya ce an fara amfani da ayyuka 32 daga cikin manyan ayyukan kimiyya da fasaha na kasa guda 77 da aka tsara.
Haka kuma, ana kafa cibiyoyin binciken bangaren injiniya da fasahohin kasuwanci da kirkire-kirkiren bangare a masana’antu, a fadin kasar. (Fa’iza)