Da yammacin yau Laraba 3 ga watan Satumba ne, kasar Sin ta karbi bakuncin bikin nishadantarwa, watau bikin gala na cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar ta Sin kan zaluncin Japanawa da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin kuma ya kalli shagulgulan da aka gudanar.
Bikin nishadantarwar na gala ya fi mayar da hankali ne kan muhimman abubuwan da suka faru a tarihi da kuma lokutan da suka kasance na fagen fama ga kasar Sin a matsayin babban filin da ake gumurzu a yankin gabashin duniya lokacin yaki da mulkin danniya a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp