Manzon musammam na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a yankin kahon Afrika, Xue Bing, ya jaddada matsayar kasar Sin ta ci gaba da taimakawa kokarin kasashen yankin kahon Afrika ta fuskar tsaro da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Manzon na kasar Sin ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin da Sin da kasashen suka kaddamar da taronsu na farko, kan zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci da ci gaba.
Xue Bing, ya shaidawa ministoci da manyan jami’an da suka halarci taron a birnin Addis Ababa na Habasha cewa, kasar Sin za ta ci gaba da marawa kasashen yankin baya, domin daukaka cikakken burinsu na bai daya na tabbatar da tsaro mai dorewa da kiyaye zaman lafiya da tsaron yankin da ajiye makamai.
Taron na yini biyu da aka kammala jiya Talata, ya samu halartar ministoci da manyan wakilai daga kasashen yankin kahon Afrika da suka hada da Habasha da Kenya da Sudan da Sudan ta Kudu da Somaliya da Uganda da Djibouti. (Fa’iza Mustapha)