A kwanan nan ne dai aka gudanar da taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU karo na 38, inda aka zabi ministan harkokin wajen kasar Djibouti Mahmoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar AU na tsawon shekaru hudu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya taya shi murna a yau 17 ga wata, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da Youssouf, da sabuwar hukumar gudanarwa ta AU.
Yayin da yake amsa tambayoyi a gun taron manema labaru na yau, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kasar Sin tana kallon dangantakarta da AU daga mahanga mai muhimmanci kuma na dogon lokaci. Yana mai cewa “A halin yanzu, zaman lafiya da ci gaba a Afirka na fuskantar sabbin damammaki da kalubale, kuma kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da shugaba Mahmoud Ali Youssouf da sabuwar hukumar ta AU, da ci gaba da nuna goyon baya ga kungiyar AU wajen taka muhimmiyar rawa don aiwatar da dunkulewar kasashen Afirka, da samar da murya mai karfi a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, tare da sa kaimi ga raya zurfafar dangantakar dake tsakanin Sin da AU, da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, da jagorantar hadin kan kasashe masu tasowa don inganta kai da sa kaimi ga zamanantarwa tare. (Mohammed Yahaya)