Wakilin musammam na gwamnatin kasar Sin kan harkokin Turai da Asiya Li Hui, ya ziyarci kasashen Ukraine da Poland da Faransa da Jamus da hedkwatar kungiyar Tarayyar Turai EU da kuma Rasha, daga ranar 15 zuwa 26 ga wata.
Da take gabatar da ziyarar yayin taron manema labarai na yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce Li Hui ya yi tuntuba mai zurfi da ma musayar ra’ayi da dukkan bangarori, game da batun warware rikicin Ukraine a siyasance. Haka kuma, ya bayyana matsayin kasar Sin da shawarwarinta, da sauraron ra’ayoyi da shawarwarin dukkan bangarorin tare da kara samun matsayar kasashen duniya.
A cewar Mao Ning, dukkan bangarorin sun dauki ziyarar ta Li Hui da muhimmanci matuka, kana sun yaba da kyakkyawar rawar da Sin ke takawa wajen inganta tattaunawar zaman lafiya da kiran da ta ke yi na a girmama cikkaken ‘yanci da ikon kasashe da kuma kiyaye manufofi da ka’idojin MDD, suna kuma sa ran ganin Sin ta ci gaba da yin kyakkyawan tasiri. (Fa’iza)