Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, a gun taron koli kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a ranar 24 ga watan nan, inda ya gabatar da wasu shawarwari guda uku kan daidaita yanayin duniya, tare da sanar da gudummawar kasarsa dangane da tunkarar sauyin yanayi nan zuwa shekara ta 2035, al’amarin da ya samu babban yabo daga sassan kasa da kasa.
Kafar watsa labarai ta BBC ta kasar Birtaniya na ganin burin kasar Sin a fannin rage fitar da iska mai gurbata yanayi a matsayin “alkawari mai matukar ma’ana”.
Shugaba Xi ya yi kira ga bangarori daban-daban da su nuna karfin zuciya, da daukar nauyin dake wuyansu, tare kuma da zurfafa hadin-gwiwa a fannin tinkarar matsalolin yanayi a duniya, al’amarin da ya kafa sabuwar alkibla ga ayyukan shawo kan kalubalen sauyin yanayi.
A sabuwar gudummawar da shugaba Xi ya sanar da cewa kasarsa za ta bayar dangane da tunkarar sauyin yanayi nan zuwa shekara ta 2035, a karo na farko ya bayyana aniyar kasar Sin ta rage fitar da nau’o’in hayaki masu dumama yanayi, daga matsayinsu na koli zuwa tsakanin kaso bakwai zuwa kaso goma bisa dari nan zuwa shekarar 2035, wanda ya shafi dukkan fannonin tattalin arziki, da dukkan nau’o’in iska masu gurbata muhalli. Irin wannan aniya ta kasar Sin ta zama abun koyi ga duk duniya baki daya. Al’amarin da zai kuma karfafa gwiwar sassan kasa da kasa wajen tinkarar kalubalen sauyin yanayi.
Ka’idar aikin bai daya amma bisa mabambantan nauyi, babban tushe ne na inganta matakan shawo kan matsalolin yanayin duniya. A matsayinta na kasar dake da babbar niyya, da daukar matakai masu karfi, da kuma aiwatar da su a zahirance, Sin za ta yi bakin kokarinta wajen cimma sabon burinta a fannin tinkarar kalubalen sauyin yanayi. (Murtala Zhang)