• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Nace Kan Ra’ayin Hadin Gwiwa Na Hakika A Taron G20 A Indonesia

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira a yau Juma’a ga kasashen duniya a tsibirin Bali na kasar Indonesia, da su tsaya tsayin daka kan hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, da raya hulda mai inganci a wannan lokaci mai cike da kalubaloli.

Wang ya bayyana hakan ne a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar G20 da aka gudanar a tsibirin Bali na kasar Indonesia.

  • Karin Kamfanoni Za Su Halarci Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Amfani Da Su Na Kasa Da Kasa Na Kasar Sin

Wang Yi ya ce, da farko, ya kamata kasashe su kasance abokan hulda tare da mutunta juna da tuntubar juna bisa daidaito. Kamata ya yi a tafiyar da harkokin kasa da kasa ta hanyar tuntubar juna tsakanin kasashe, kana a kiyaye dokokin kasa da kasa cikin hadin gwiwa.

Na biyu, ya kamata kasashe su kasance abokan zaman tare cikin lumana da hadin gwiwar moriyar juna. Yana mai cewa, sai wata kasa ta mutunta tsaron wasu kuma ta kiyaye tsaron kowa ne, kafin ta iya samun nata tsaro na hakika.

Wang ya kara da cewa, yadda wata kasa ta fifita tsaronta a kan tsaron sauran kasashe da kuma karfafa kawancen soji, na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin kasashen duniya, da kuma sanya kanta cikin rashin kwanciyar hankali.

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Kana na uku, ya kamata kasashe su kasance abokan hadin gwiwa ba tare da wata rufa-rufa ba, da damawa da kowa, da yin cudanya da juna.

Wang ya ce, ya kamata takara tsakanin kasa da kasa ta kasance mai adalci, kuma bai kamata ta zama mummunar gasa ba ko ma yin fito na fito da juna.(Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik
Daga Birnin Sin

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki
Daga Birnin Sin

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
Next Post
Gwamnonin APC Sun Kutsa Kai Jihar Ribas Suna Kokarin Farauto Wike Cikin Jam’iyyarsu

Gwamnonin APC Sun Kutsa Kai Jihar Ribas Suna Kokarin Farauto Wike Cikin Jam'iyyarsu

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.