Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD ya bayyanawa taron kwamitin sulhu na MDD kan batun kasar Afirka ta Tsakiya jiya Talata cewa, yanzu Afirka ta Tsakiya tana cikin wani muhimmin lokaci na shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin dogon lokaci, don haka wajibi ne kasashen duniya su kara taimakawa kasar.
A yayin taron, jakadan kasar Sin ya ce, da farko wajibi ne a aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya daga dukkan fannoni. Na biyu, wajibi ne a dakile barazanar da kungiyoyin ’yan bindiga suke haifarwa.
Na uku, dole ne a goyi bayan rundunar tabbatar da zaman lafiya ta MDD dake Afirka ta Tsakiya wajen kara taka rawa. Na hudu, wajibi ne a mara wa Afirka ta Tsakiya baya wajen sake gina kasa.
Kasar Sin tana son ci gaba da hada kai da ragowar kasashen duniya, don kara goyon bayan Afirka ta Tsakiya ta fuskar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar. (Tasallah Yuan)