Wakilin dindidin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga kasa da kasa su hada hannu wajen inganta raya harkokin da suka shafi mata.
Fu Cong ya yi kiran ne yayin muhawara ta shekara-shekara ta Kwamitin Sulhu na MDD kan batutuwan da suka shafi mata da tsaro da zaman lafiya. Ya ce yanzu haka, duniya na cikin wani yanayi na tangal-tangal. Kuma har yanzu mata na fuskantar rikici da wariya da rashin daidaito ta fuskar tattalin arziki. Ya ce kare hakkoki da muradun mata da raya harkokin da suka shafe su, na bukatar kasa da kasa su karfafa hadin gwiwa domin yunkurawa tare.
Ya ce da farko, kamata ya yi a yi kokarin inganta karewa da warware rikice-rikice. Na biyu, ya kamata a ba da goyon baya ga karfafa gwiwar mata. Na uku, ya zama wajibi a inganta musaya da hadin gwiwa a bangarorin da suka shafi mata.
A cewarsa, kasar Sin na gab da sake karbar bakuncin taron mata na duniya a Beijing, domin cimma matsaya kan hadin gwiwa da hadin kai, da hada karfi da karfe wajen shawo kan kalubale da karfafa raya harkokin da suka shafi mata. (Fa’iza Mustapha)