Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce ya kamata kasashen duniya su taimakawa bangarorin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, wajen inganta shirye-shiryen zabuka da kaucewa tsoma baki cikin harkokin gidan kasar.
Fu Cong ya bayyana haka ne jiya Alhamis, yayin taron Kwamitin Sulhu na majalisar kan ayyukan shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya (MINUSCA).
- Jirgin Saman Da Kasar Sin Ta Kera Mai Amfani Da Lantarki Ya Yi Tashin Farko Cikin Nasara
- Jirgin Saman Da Kasar Sin Ta Kera Mai Amfani Da Lantarki Ya Yi Tashin Farko Cikin Nasara
A cewarsa, yanzu haka, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na cikin kyakkyawan yanayi, kuma an samu nasara wajen inganta karfin gwamnati tare da samun ci gaba a tsarin wanzar da zaman lafiya a siyasance.
Da yake bayyana dukkan dabarun shirya gudanar da zabuka a kasar a matsayin muhimmin matakin karfafa zaman lafiya, ya kuma ce ya kamata ya zama wata dama ga kasar ta hawa tafarkin samun zaman lafiya da ci gaba da wadata. Fu Cong ya kuma yi kira ga shirin MINUSCA da ya dauki batun goyon bayan shirye-shiryen zabukan da muhimmanci, yana bukatar dukkan bangarori su cimma matsaya guda ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa game da wasu shirye-shiryen da suka shafi zabukan.
Ya kara da cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar na da tasiri kan kasashe makwabta, yana mai kira ga kasashen duniya su mayar da hankali ga yaduwar mummunan tasirin rikicin Sudan da taimakawa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya karfafa karfinta na tsaro da tsaron iyakoki da ma kwanciyar hankalin yankin baki daya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp