Kasar Sin ta yi watsi da ikirarin Amurka dake neman rage barazana maimakon mayar da Sin saniyar ware, tana mai cewa, ainihin barazanar da duniya ke fuskanta ita ce sabon yakin cacar baka.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana hakan, tana mai jaddada muhimmancin bayyana ma’anar barazana.
A cewarta, kasar Sin na neman bude kofa da samar da yanayin kasuwanci da ya kai mizanin kasa da kasa wanda zai dace da bukatun kasuwa kuma bisa dokoki ga dukkan harkokin kasuwanci daga fadin duniya. Ta ce kasar Sin na hadin gwiwa da zuba jari a bangarorin da suka shafi tattalin arziki da cinikayya da kimiyya da fasaha da sauran kasashe, bisa mutunta juna da moriyar juna da ma samun sakamako na bai daya. Don haka, wannan kasar Sin din ba ta zaman barazana sai ma gabatar da damarmaki.
Kakakin ta kuma jaddada cewa, ainihin barazanar da duniya ke fuskanta ita ce fito-na-fito ko kuma sabon yakin cacar baka domin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe da haifar da tashin hankali da rikici a shiyyoyi da siyasantar da batutuwan tattalin arziki da cinikayya da fasahohi da kawo tsaiko ga tsarin sarrafawa da samar da kayayyaki da kuma tura barazanar tattalin arziki da matsalolin kudi da wata kasa ke fama da su, kan sauran kasashe domin cin gajiyar arzikin duniya a wani yanayi na zagaye. (Fa’iza)