A jiya ne, ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar da sabbin bayanai game da masana’antar kera jiragen ruwa ta kasar. Dangane da manyan alkaluma uku da suka hada da aikin kera jiragen ruwa, da wadanda aka karbi odarsu, da wadanda ke jira a karbi odar su, kasar Sin ta kasance a kan gaba a duniya wajen samar da kayayyakin aikin kera jiragen ruwa tsawon shekaru 14 a jere. A karon farko, hannayen jarinta a kasuwannin duniya, ya zarce kashi 50 cikin 100.
Bayanai sun nuna cewa, a shekarar 2023, aikin kera jiragen ruwa na kasar Sin, ya kai tan miliyan 42.32, wanda ya karu da kashi 11.8 bisa 100 kan makamancin lokacin shekarar 2022. Yawan sabbin oda ya kai tan miliyan 71.2, wato ya karu da kashi 56.4 cikin kari bisa na shekarar 2022. Ya zuwa karshen shekarar 2023, adadin odar da aka karba, ya kai tan miliyan 139.39, karuwar kashi 32.0 cikin 100 kan na shekarar 2022. (Ibrahim Yaya)