Alkaluman da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar a ranar Talata sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Yuni, adadin tashoshin 5G na kasar ya karu zuwa kusan miliyan 3.92.
Alkaluman sun nuna cewa, adadin karuwar tashoshin na 5G ya kai 540,000 tun karshen shekarar da ta gabata zuwa karshen watan Yuni, wanda ya kai kashi 33 cikin dari na adadin tashoshin wayar salula a fadin kasar baki daya.
Adadin masu amfani da wayar salula ta 5G a kasar shi ma ya karu da miliyan 105 daga karshen shekarar da ta gabata, gaba daya ya kai miliyan 927 a karshen watan Yunin bana. (Mai fassara: Yahaya)