Gwamnatin jihar Kano ta sayi takin zamani na Naira Biliyan 6.2. domin rabawa manoma da nufin bunkasa noma a jihar.
Kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar, Dr. Danjuma Mahmoud ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Kano.
- Yarjejeniyar Beijing: Mabudin Zaman Lafiya A Zirin Gaza
- Majalisa Ta Nemi A Kori Shugaban Hukumar NMDPRA Kan Zargin Rashin Ingancin Matatar Dangote
Mahmoud ya ce, an riga an raba tireloli 52 dauke da taki na Naira biliyan 1.2 ga manoman kananan hukumomin jihar 44 kyauta.
Ya ce, gwamnatin jihar ta sayo tireloli 180 na takin zamani da kudinsu ya kai Naira biliyan 5 domin rabawa manoma a kan rangwamen kashi 50 cikin 100.
Kwamishinan ya ce, an sayo takin ne daga Kamfanin Samar da kayan Aikin Noma na Jihar Kano, amma “an sake inganta su” domin samun dimbin amfanin noma.
Ya ce, an tura kwararrun ma’aikata 440 zuwa kananan hukumomi 44 na jihar domin fadakar da manoma yadda za a yi amfani da sabbin irin shuka da aka samo.
Kwamishinan ya kara da cewa, an ware kadada 1,299 a dajin Dansoshiya domin bunkasa noman rani a jihar.
A cewarsa, gwamnatin jihar tana aikin gyaran madatsun ruwa guda 20 da suka hada da dam din Kafinchiri domin bunkasa noman rani a jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara aikin gina titunan karkara domin saukaka fitar da amfanin gona bayan girbi.
Talla